Ana sace dukiyar cin hancin da gwamnati ta kwato a Najeriya – CITAD

Shugaban Cibiyar bunkasa fasaha ta CITAD a Najeriya, Dr Yunusa Zakari Ya’u yayi zargin cewar ikrarin yaki da cin hanci da rashawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari keyi na samun tasgaro saboda yadda ake sace dukiyar da aka kwato.

Ya’u yace duk da makudan kudaden da gwamnatin tayi nasarar kwatowa, shirin na fama da matsalar siyasa, yayin da kuma ake ci gaba da sace dukiyar da aka kwato daga barayin gwamnati.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban Cibiyar CITAD dake jawabi wajen wani taro a Kano na cewar, daya daga cikin matsalolin da gwamnatin Buhari ke fuskanta wajen yakin shine siyasantar da yakin da kuma sanya wasu mutane a gaba, yayin da shi kadai ne ke bayyana abinda ake kira cin hanci da kuma masu aikata laifin.

Jami’an hukumar EFCC na gudanar da aikin su Daily Post

Ya’u yace yanzu haka akasarin ‘Yan Najeriya sun dauka cewar an yafe wa mutanen da ake zargi da rub-da-ciki da kudaden talakawan kasar da suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki.

Jami’in yace akwai kuma shirin sasantawa da mutanen da suka saci dukiyar talakawa ta hanyar tattaunawa tsakanin su da hukumomin dake yakin, matakin da ya kaiga karbo biliyoyin nairori ba tare da kai su kotu na ba, amma kuma yace babu wanda ya san inda wadannan kudade suka shiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *