Yau ake saran Olaf Scholz ya karbi ragamar jagorancin kasar Jamus, abinda zai kawo karshen mulkin shekaru 16 da Angela Merkel keyi da kuma bude wani sabon babi a tarihin kasar.
Wannan zai gudana ne bayan da Majalisar Bendestag ta tabbatar masa da mukamin, daga bisani kuma shugaban kasa Frank-Walter Steinmeier ya rantsar da shi.
Scholz ya rike mukamin ministan kudi a karkashin gwamnatin Merkel kafin samun nasarar zaben da yayi a ranar 26 ga watan Satumbar da ta gabata.

Sabon shugaban gwamnatin mai shekaru 63 yayi nasarar kulla yarjejeniyar kawancen kafa gwamnati na shekaru 4 da wasu jam’iyyun siyasar kasar, yayin da ya bayyana farin cikin sa da fahimtar junar da suka samu.
Scholz ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar sa ta ’Social Democrat‘ a shekarar 1980, amma sai ya gaza jagoracin ta a matsayin shugaba saboda zargin da ake masa na kin goyan bayan manufofin ta sau da kafa.
Well done Mr Olaf schoz congratulations