Wata babbar mota ta kashe dalibai 13 a Lagos

Akalla daliban makarantu 13 ake fargabar sun mutu yau a birnin Lagos dake Najeriya lokacin da wani direban babbar mota ya afka musu bayan sun tashi daga makaranta.

Bayanan dake zuwa mana na nuna cewar, an samu hadarin ne akan hanyar Isheri dake kusa da tashar ’Yan Sandan Ojodu, abinda ya haifar da katse zirga zirgan ababan hawa a hanyar da kuma boren matasa.

Wasu shaidun gani da ido sun ce katsewar birki ne yayi sanadiyar samun hadarin, yayin da direbar motar yayi kokarin tserewa bayan aukuwar lamarin.

Matasan cikin fushi sun kai hari ofishin ‘Yan Sandan Ojodu wadanda suka kama direbar motar suka tsare shi, abinda ya sa su amfani da hayaki mai sa hawaye da harsashin roba domin tarwatsa su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *