Mutane miliyan 23 za su fuskanci matsalar karancin Abinci a Afrika- rahoto

Cibiyar da ke da kula da abinci ta nahiyar Afrika ta ce matsalar karancin abinci na ci gaba da girmama a yankin Sahel, da kasashen yankin yammacin Afrika, inda yanzu haka kimanin mutane miliyan 23 da dubu 700 kwatankwacin kashi 7.4 na al’ummar kasashe 15 da aka nazarta ke cikin matsalar.

Wannan adadi dai na iya karuwa a wannan lokaci na tsakanin rani da damina kamar yadda alkaluman cibiyar suka nuna cikin wani rahoton karshen shekara da ta fitar.

Kimanin mutane miliyan 33 da dubu dari 4 ne za su iya fadawa cikin matsananciyar barazanar karancin abinci idan har ba a dauki wasu matakai na gaggawa ba, a cewar wata kwararriya daga cibiyar wadda ke taronta ta hoton bidiyo.

Jami’ar ta ce adadin na wakiltar kashi 10.5 na al’ummomin kasashen.

Laurent Bossard babban daraktan cibiyar hadakar kasashen sahel da na yammacin afrika (CSAO), ya ce babban dalilin faruwar matsalar karancin abincin ita ce, rashin tsaro da tashe tashen hankulla da yankin ke fama da shi 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *