Mbappe ya goge tarihin da Messi ya kafa a gasar zakarun Turai

Dan wasan gaba na PSG Kylian Mbappe ya goge tarihin Lionel Messi bayan zama dan wasa mafi yarinta da ya zura kwallaye 31 karkashin gasar cin kofin zakarun Turai.

Mbappe dan Faransa mai shekaru 22 ya kafa tarihin ne bayan kwallayensa biyu a ragar Club Brugges yayin haduwar kungiyoyin biyu a daren jiya.

A mintuna 7 na farkon wasan na jiya ne Mbappe ya zura kwallaye 2 gabanin ya taimakawa Messi ya kara kwallo guda a minti na 37 kana PSG ta samu bugun fenariti da ya kaita ga nasarar ta kwallaye 4 da 1 kan Club Brugge.

Kafin nasarar ta jiya dai Messi ke da tarihin zura kwallaye 30 a karkashin gasar tun yana da shekaru 23 amma kuma yanzu Mbappe ya goge tarihin tare da zamowa dan wasa mafi karancin shekaru da ya kai ga nasarar zura kwallaye 31 a gasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *