Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta kafa tarihin shiga sahun kungiyoyin da suka kammala wasannin rukuni na gasar cin kofin zakarun Turai ba tare da rashin nasara ko da a wasa guda ba, bayan nasararta kan AC Milan da kwallaye 2 da 1.
Yayin wasan na jiya, wanda zakaran Liverpool Mohamed Salah ya nuna bajinta kwarai, Milan ta fara zura kwallo ta hannun dan wasanta Fikayo Tomori tun a minti na 28 da fara wasa sakamakon kuskuren da mai tsaron ragar Reds Alisson Becker ya yi, amma kuma Mohammed Salah ya farke a minti na 36 kana Origi ya kara guda a minti na 55 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Kwallon da Salah ya zura a jiya ta zama kwallo ta 20 cikin wannan kaka kadai daya kunshi 7 karkashin gasar ta cin kofin zakarun turai, wanda ke nuna shi ne dan wasan Liverpool na biyu tun bayan Ian Rush da ya nuna wannan makamanciyar bajinta.
A bangare guda shi ma Origi kwallon tasa ta jiya ita ce ta farko da dan wasan ya zurawa kungiyar tasa tun bayan ta wasan karshe na makamanciyar gasar a 2019 lokacin da Liverpool ta doke Tottenham tare da dage kofin gasar.