Jami’an ‘yansandan Faransa sun sanar da kame wani mutum da ke cikin tawagar Saudiyya da ake da zargi da yiwa dan jarida Jamal Kashoggi kisan gilla a Turkiya cikin shekarar 2018.
A yammacin yau talata ne jami’an ‘yan sandan kan iyaka na Faransa suka kame Khalid Alotaibi mai shekaru 33 biyo bayan umarnin kamensa da Turkiyya ta bayar.
Majiyoyin shari’a a Faransa sun ce an kame Alotaibi ne lokacin da ya ke kokarin hawa jirgi zuwa birnin Riyadh na Saudiyya a babban filin jirgin saman a Charles de Gaulle da ke Paris, yayinda zai gurfana gaban shari’a kowanne lokaci a gobe laraba.
A shekarar 2020 ne Turkiya ta fara wasu mutum 20 da ake zargin hannunsu a kisan na Kashoggi ba tare da halartarsu gaban kotu ba, ciki har da tsaffin hadiman Mohammed bin Salman yarima mai jiran gadon sarautar saudiyya 2.
Haka zalika a cikin shekarar nan Turkiya ta kara wasu mutum 6 cikin wadanda ake zargi da kisan dan jaridar na Saudiya Jamal Kashoggi suma dai ba tare da sun je kasar ta Turkiya ba.