Tsagerun yan bindiga sun sake tasa keyar dandazon mutane a jihar Kaduna

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wasu tsagerun yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari ƙauyukan karamar hukumar Birnin Gwari, dake jihar Kaduna.

Rahotannin da muka samu sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da sama da mutum 36 zuwa wani ɓoyayyen wuri a cikin jeji.

Yan bindigan sun kai waɗan nan hare-haren ne a ranar Lahadi da kuma safiyar ranar Litinin da suka gabata.

Ɗaya daga cikin mutanen da maharan suka yi kokarin sacewa ya kuɓuta, Malam Muhammad, ya tabbatar da cewa maharan sun tasa keyar mata, kananan yara da sauran su.

Cikakken bayani na nan tafe…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *