Tilastawa mutane yin rigakafin Korona kamar aikata laifin yaki ne – McGregor

Fitaccen dan wasan dambe na komai da ruwanka da ake amfani da hannu da kafa cikinsa da aka fi sani da UFC a turance, Conor McGregor, ya ce tilastawa mutane yin allurar rigakafin cutar Korona tamkar aikata laifin yaki ne.

Dan damben na UFC da ke wakiltar kasar Ireland ya bayyana haka ne a shafinsa na twitter, koda yake bai bayyana ra’ayin zai karbi allurar rigakafin Koronar ba, ba ko kuma a’a.

A cewar McGregor, ba zai yadda da shirin kungiyar Tarayyar Turai na tilastawa mutane karbar rigakafi ba, amma ya san wadanda ke shugabantarsu za su aiwatar da umarnin da aka ba su ko da jama’a ba sa so, dan haka lokaci ya yi da kasar Ireland za ta fice daga cikin kungiyar Tarayyar Turai.

Wannan ra’ayi na MacGregor dai ya janyo masa caccaka daga sassa da dama, abinda ya sanya shi sake wallafa sako a shafin nasa na twitter da ke cewar ba wai yana adawa da alluran rigakafin Korona bane, yana adawa ne da dakilewa mutane ‘yancinsu na zabin yi ko kuma akasin haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *