Mutane 38 sun mutu 69 sun jikkata a gobarar gidan Yarin Burundi

Mutane 38 sun mutu sakamakon wata gobara da ta barke a wani gidan Yari mai cike da cinkoson fursunoni a Burundi yau Talata.

Yayin tabbatar da alkaluman ga manema labarai, mataimakin shugaban kasar ta Burundi Prosper Bazombanza, ya ce baya ga wadanda suka mutu, wasu mutanen 69 kuma sun samu munanan raunuka sakamakon gobarar da ta tashi a ginin da ke Gitega babban birnin siyasar kasar a gabashin Afirka.

Bayanai sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 4 na safe a kasar ta Burundi, inda wutar ta lalata wurare da dama na ginin gidan Yarin.

Kawo yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba, wadda aka samu nasarar kashe ta, zalika babu wani bayani a hukumance kan lamarin.

Gidan Yarin na birnin Gitega na dauke da fursunoni sama da dubu 1 da 500 zuwa karshen watan Nuwamban da ya kare, adadin da ya zarce yawan fursunoni 400 da ya kamata ya dauka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *