Kungiyar Barcelona na fuskantar hatsarin tafka hasarar miliyoyin euro idan har ta yi rashin nasarar tsallakawa zuwa zagayen na biyu a gasar zakarun Turai yayin karawar ta Bayern Munich a Jamus.
Barcelona ta tsinci kanta cikin tsaka mai wuya ce la’akari da cewar ita ce ta biyu a rukuni na 5 da maki 7, maki 8 tsakaninta da Bayern Munich, sai dai kuma tsakaninta da ta 3 wato Benfica maki 2 ne kacal, wadda ita kuma za ta kara da Dynamo Kyiv, wasannin da dukkaninsu za a buga a ranar Laraba 8 ga watan Disamba.
Cikin kasafin kudinsu na kakar wasa ta bana, hukumar gudanarwar Barcelona ta tsara kasafin cewa za ta kai akalla zagayen kwata final a gasar Zakarun Turai, abinda ya sanya ficewarta daga gasar a matakin rukuni zai janyo mata hasarar euro miliyan 20 da dubu 200.
Sai dai kungiyar za ta iya rage hasarar idan ta yi kokarin lashe gasar Europar da take fuskantar hatasarin hantsilawa cikinta, domin idan ta dage kofin za ta lashe kyautar euro miliyan 14 da dubu 900.