Luguden jiragen NAF ya yi ajalin kwamandan ISWAP, Abou Sufyan

Shiryayyun luguden da jiragen saman sojojin Najeriya suka yi ya kawo karshen gagararren dan ta’addan kwamandan ISWAP, Abou Sufyan tare da wasu mayakansa a kusa da tafkin Chadi da ke jihar Borno.

PRNigeria tattaro cewa, luguden ruwan wutan da rundunar sojin saman Najeriya ta kaddamar karkashin Operation Hadin Kai ta yi shi ne a ranar Lahadi daidai da wurin da miyagun ke adana makamansu a Kusama da Sigir da ke karamar hukumar Marte a jihar Borno.

Aikin sintiri tare da dubawa da kuma saisatawa da sojojin suka yi, ya bayyana cewa akwai mayakan ta’addancin masu yawa da suka taru a yankin domin shirya kaddamar da farmaki kan sojojin yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *