Akalla fararen hula hudu ne suka mutu yayin da wasu hudu suka jikkata a ranar Talata, sakamakon wani harin bam da aka kai da babur a kusa da wani asibiti da ke tsakiyar birnin Basra a kudancin kasar Iraqi.
Kawo yanzu dai babu wanda ya yi ikirarin kai harin a birnin na na Basra, wanda a shekarun baya-bayan ya sha fama da hare-hare.
Sai dai a makwannin da suka gabata an kai munanan hare-hare kan mayakan Kurdawa a arewacin Iraqi, wadanda IS ke ikirarin kaiwa.
Hare-haren ta’addanci da kuma tsananin yaki sun tagayyara kasar Iraqi tsawon shekaru tun bayan da Amurka ta mamaye kasar tare da kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar marigayi Saddam Hussein a shekara ta 2003.

Idan za a iya tunawa dai, IS ta taba kafa shugabancinta a yankuna masu fadi da ke Syria da Iraki daga shekara ta 2014, amma daga bisani yankunan suka kubuce mata, sakamakon murkushe kungiyar da dakarun sojin Iraqi suka yi tare da taimakon Amurka da kungiyar tsaro ta NATO.