Wani jami’in dan sandan kasar Kenya ya harbe mutane shida har lahira, ciki har da matarsa, tare da jikkata wasu biyu kafin daga bisani ya harbe kansa da bindiga.
Tuni dai lamarin ya haifar da zanga-zangar da fusatattun mazauna yankin marasa galihu a birnin Nairobi suka rufe hanya da kona tayoyi.
Binciken ‘yan sanda ya gano cewar, jami’in nasu y afara harbin matarsa a wuya da bindiga kirar AK-47, kafin ya budewa sauran jama’ar dake kusa wuta, nan take kuma ya kashe mutane 6 kafin ya kashe kansa.
A bangaren wadanda suka jikkata kuma, an kwantar da wasu mutane biyu a asibiti.
Har yanzu dai ba a tantance dalilin ya sanya dan sandan Kenyan tafka wannan ta’asa ba, said ai wata majiya ta ce jami’in da matarsa sun dade suna samun rashin fahimtar juna.