Hukumomin Najeriya sun sanar da kama fursinoni 21 daga cikin 262 da suka tsere daga gidan yarin Jos, lokacin da wasu ‘Yan bindiga suka kai hari.
Mai magana da yawun gidan yarin Jihar Filato Geofrey Longdiem ya sanar da kama fursinonin 21 daga cikin wadanda suka tsere ranar 28 ga watan Nuwamba, yayin da kakakin rundunar Gandirobobin dake kula da gidajen yarin na kasa Francis Enobore yace mutane 10 sun mutu sakamakon artabun da akayi tsakanin ‘Yan bindigar da jami’an tsaro lokacin da suka kai harin.
Longdiem yace daga cikin fursinonin 21 da aka kama, guda biyu mahaifiyar su ce ta kai su domin kammala hukuncin da kotu ta yanke musu.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato tace yayin da wasu fursinoni suka tsere daga gidan yarin sakamakon harin, an ritsa da wasu ‘Yan bindiga daga cikin maharan, amma kuma babu wani karin bayani dangane da abinda ya faru da su.
Gidan yarin Jos na dauke da fursinoni 1,060 lokacin da aka kai harin, kuma 560 daga cikin su wadanda suke jiran a yanke musu hukunci ne, yayin da 500 kuma ke cin sarka.
A wani hari makamancin wannan a watan Yuli, fursinoni 4 suka tsere daga gidan yarin na Jos, abinda ke nuna matsalar tsaron da ake fama da shi gidan.
Adadin firsinoni 262 da suka gudu daga gidan yarin Jos ya kawo jimillar fursinoni 5,238 da suka tsere daga gidajen yari daban daban dake Najeriya a cikin shekara guda.
Baya ga gidan yarin Jos an samu irin wannan matsalar a gidajen yarin Jihohin Edo da Imo da kuma Kogi, abinda yayi sanadiyar tserewar fursinoni da dama.