An bude bikin baje kolin fina finai na duniya a kasar Saudi Arabiya

Kasa da shekaru 4 bayan cire haramcin zuwa gidajen sinima da gwamnatin Saudi Arabia tayi, kasar ta shirya wani kasaitaccen biki a birnin Jeddah domin karrama fitattun masu shirin fina finan duniya irin sa na farko a tarihin kasar.

Masu shirin fina finai daga Saudi Arabiya da kasashen Larabawa da kuma kasashen duniya suka mamaye wurin bikin, wasu daga cikin su sanye da kayan kawa irin na kasashen duniya sabanin abayar da aka saba ganin matan Larabawa suna sanyawa.

Daraktan shirya bikin Mohammed Al Turki ya bayyana yau a matsayin babbar ranar tarihi ga Masarautar Saudiya.

Mota kirar marsandi da Lewis Hamilton yayi tsere da ita a gasar Saudi Arabiya ANDREJ ISAKOVIC POOL/AFP

Ita dai Saudi Arabiya ta haramta gidajen nuna fina finai ko kuma sinima na shekaru da dama, har sai a watan Afrilun shekarar 2018 aka bude su ga jama’a.

Yayin gudanar da wannan biki da bude yau, ana saran masu shirin fina finan da daraktoci zasu kwashe kwanaki 10 suna nuna bajintar su a birnin Jeddah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *