Amurka ta kauracewa wasannin Olympics da za a yi a China

Amurka ta ce jami’anta ba za su halarci gasar Olympics a Beijing da za ta gudana cikin shekarar 2022 dake tafe ba.

Sakataren yada labaran fadar White House Jen Psaki, ya ce ‘yan wasan Amurka za su fafata a wasannin gasar, sai dai kauracewar diflomasiyar na nufin babu wani jami’in gwamnati da zai halarci taron, sakamakon yadda gwamnatin China ke ci gaba da yin kisan kare dangi da cin zarafin bil’adama a yankin Xinjiang.

Tuni dai gwamnatin China ta yi Allah wadai da matakin da shugaba Biden ya dauka, inda ministan harkokin wajen kasar Zhao Lijian, ya shaidawa taron manema labarai cewa, gasar Olympics din da za su karbi bakunci ba dandali bane na siyasa, dan haka babu dalilin da zai sanya Amurka daukar matakin hana jami’anta halartar kallon gasar.

Kasashe da dama ne dai ke yin tir da take hakkin dan Adam da suke zargin kasar Sin dai yi kan ‘yan Kabilar Uighur, inda mambobin majalisar Tarayyar Turai ke kira da a kauracewa zuwa gasar ta Olympics.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *