‘Yan bindiga sun saki mambobin Cocin Baptist fiye da 60 a Kaduna

‘Yan bindiga sun saki mambobin Cocin Baptist 61 dake Kakau Daji a Kaduna bayan shafe wata daya suna garkuwa da su.

Da yammacin ranar Juma’ar nan da ta gabata ne, shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN reshen Jihar ta Kaduna, Joseph Hayab ya tabbatar da sako mutanen.

Yayin karin bayani a jiya Asabar Hayab y ace tun da farko sai da ‘yan bindigar suka nemi a basu kusan naira miliyan 100 kafin sakin wadanda suka yi garkuwar dasu, said ai bai yi karin bayan kan ko an biya kudaden ba.

A ranar 31 ga watan Oktoban da ya gabata, gungun ‘yan bindigar suka kai farmaki kan Cocin na Baptist dake karamar hukumar Chikun inda suka yin awon gaba da mutane 66, inda daga bisani suka kashe 2 daga cikinsu, wasu uku kuma suka sake su saboda rashin lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *