‘Yan bindiga sun kai hari kan wasu kayukan jihar Katsina

Rahotanni daga jihar Katsina a Najeriya sun ce, akalla mutane hudu suka rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata, bayan da ‘yan bindiga suka kai farmaki kan kauyukan Daurawa da Gidan Gadi da kuma Dugara, dukkaninsu a karamar hukumar Matazu.

Jaridar daily Trust da ake wallafa ta a Najeriya ta ruwaito cewar, maharan sun afkawa kauyen ne a daren Juma’ar da ta gabata da misalin karfe 10 na dare,

Wasu mazauna garin sun bayyana cewar ‘yan bindigar sun mamaye kauyukan da muggan makamai tare da lalata gidaje da dama yayin hare-haren.

Sai dai lokacin da aka rundunar ‘yan sanda a jihar ta Katsina dangane da harin, ta ce ba ta samu labarin ba, wanda ba zai rasa nasaba da rashin layin sadarwa a yankunan da suka fuskanci tashin hankalin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *