‘Yan sandan Amurka sun tsare iyayen matashin nan mai shekaru 15 da ya harbe dalibai hudu a wata makarantar sakandaren Michigan bayan da ya yi amfani da bindigar da mahaifinsa ya siya, kwana guda bayan da aka tuhume su da laifin kisan kai ba da gangan ba.
‘Yan sanda suka ce sun yi nasarar kama iyayen matashin su biyu ne a wani ginin masana’anta dake Detroit – mai tazarar kilomita 40 daga wurin da aka yi harbin, kusa da inda aka gano motarsu tun farko.
Shugaban ‘yan sandan Detroit James E White ya shaida wa manema labarai cewa, “yayi mamakin kasancewarsu cikin ginin.