Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Najeriya ta amince wa Hukumar Kwallon Kafar Kasar da ta kori kocin tawagar Super Eagles Gernot Rohr tare da gaggauta dauko kwararren da zai maye gurbinsa.
Umarnin Ma’aikatar na zuwa ne bayan wata ganawa da ta gudana tsakanin Ministan Wasanni da Matasana Sunday Dare da kuma shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta kasar, Amaju Pinnick a birnin Abuja a jiya Alhamis.
Sai dai sharadin da Ministan ya bai wa NFF shi ne ta tabbatar da cewa ta biya Rohr daukacin hakkokinsa ko kuma wani kaso mai yawa daga cikin hakkopkin kafin ta dauko sabon kocin Super Eagles.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka zafafa kiraye-kirayen hukumar ta NFF da ta gaggauta sallamar kocin, saboda rashin tabuka abin kirki musamman a wasannin baya-baya nan na neman tikikin halartar gasar cin kofin duniya a Qatar.