Kotu ta amince wa dan Ghaddafi ya tsaya takarar zaben Libya

Wata kotun Libiya ta sake farfado da takarar dan tsohon shugaban kasar marigayi Ma’amar Ghaddafi wato Saiful Islam, da hukumar zaben kasar ta soke takararsa ta neman kujerar shugabancin kasar a zaben da ake shirin gudanarwa nan da makwanni 3 masu zuwa.

Yanzu haka dai dan tsohon jagoran juyin-juya halin kasar zai ci gaba da kasancewa cikin jerin yan takarar da za su fafata a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a ranar 24 ga wannan wata na Disamba, kamar yadda hukumcin kotun daukaka karar birnin Sabaha da ke yankin kudancin kasar ta ta tabbatar.

Labarin da kafofin yada labaran kasar sun ce, dan takarar da ya daukaka kara a gaban kotun yana mai kalubalantar matakin korar takararsa da hukumar zaben kasar ta yi, bisa abin da ta kira rashin dacewa a karkashin dokar kasar.                                                                                              

Saif al Islam Khadafi mai shekaru 49 a duniya a shekarar 2015 an taba yanke masa hukumcin kisa a karakashin wata mummunar shara’a kafin daga bisani ya amfana da yafiyar gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *