Gwamnatin jihar Kaduna ta Najeriya ta sanar da shirinta na sallamar malaman makaranta har su 233 saboda amfani da kwalin shedar kammala karatu na bogi.
Shugaban Kwamitin Zartaswa na Hukumar Bunkasa Ilimin Bai-Daya a jihar, Alhaji Tijjani Abullahi ya bayyana haka a ranar Alhamis a yayin wani taron manema labarai.
Abdullahi y ace, sun gano wannan adadin ne bayan kaddamar da wani aikin tantance sahihancin kwalayen malamai a cikin watan Afrilun bara.
Jami’in ya ce, sun yi haka ne da zummar tabbatar da cewa, malaman na da kwarewar da ake bukata ta karantawa.