‘Yan bindiga sun kubutar da fursunoni 250 a Jos

Akalla mutane 11 aka kashe, sannan fiye da fursunoni 250 suka tsere bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wani gidan yari da ke birnin Jos na jihar Filato ta Najeriya.

Harin da aka kaddamar a ranar Lahadin da ta gabata, shi ne na baya-bayan nan da ya yi sanadiyar tserewar fursunoni a Najeriya, kasar da ke zama mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika, inda ake yawan samun cinkoson gidajen yari.

Mai magana da yawun gidan yarin na Jos, Francis Enobore ya ce, an kashe fursunoni 9 da mahari guda da kuma jami’in tsaro guda bayan ‘yan bindigar sun kai farmakin, yayin da fursunoni 262 suka arce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *