Wata Kotu Ta Rushe Shugabancin Abdullahi Abbas Na APC a Kano

Wata babbar kotun tarayya a Abuja karkashin jagorancin Mai Shari’a Hamza Muazu ta soke zaben Shugabannin jam’iyyar APC reshen jihar Kano da bangaren gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gudanar a ranar Talata.

Alkalin kotun, Mai shari’a Hamza Muazu yace kotu ta amince da zaben da bangaren Sanata Ibrahim Shekarau suka gudanar.

Alkalin ya yanke hukuncin cewa bangaren Shekarau mai taken G-7 ya gudanar da zabe wanda kwamitin mutane 7 na APC ya sanya wa hannu.

Wadanda suka shigar da karar sun hada da Muntaka Bala Sulaiman da mambobin jam’iyyar 17,980 yayin da wadanda ake kara su ne APC, a matsayin wanda ake kara na daya, Mai Mala Buni, shugaban riko, Sen. John Akpanudoedehe sakataren jam’iyyar na kasa da kuma Hukumar zabe ta kasa kamar yadda Jaridar Politics Digest ta ruwaito.

Kotun ta ce sahihul ne duk taron da bangaren Ibrahim Shekarau ya jagoranta.

Jarida Radio

One Reply to “Wata Kotu Ta Rushe Shugabancin Abdullahi Abbas Na APC a Kano”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *