Sojin Guinea sun mayar da Conde gidan matarsa

Sojojin da ke mulki a kasar Guinea sun sanar da mayar da hambararen shugaban kasa Alpha Conde gidan matarsa da ke Conakry bayan tsare shi da suka yi tun lokacin da suka raba shi da karagar mulkin.

Sanarwar da sojojin suka yi ta kafar talabijin ta bayyana cewar, tsohon shugaban kasa Conde yanzu haka yana gidan matarsa Hadja Djene Conde.

Sanarwar sojin ta ce za su ci gaba da martaba shi a matsayinsa na tsohon shugaban kasa kamar yadda dokoin kasa suka tanada ba tare da yarda da wani matsin lamba daga ciki ko wajen kasar ba.

Tun ranar 5 ga watan Satumban bana da aka yi wa tsohon shugaban juyin mulki, aka daina jin duriyarsa sakamakon tsare shi da sojojin suka yi.

Conde ya jagorancin Guinea tun daga shekarar 2010 bayan nasarar zaben da ya samu har sau biyu, amma kuma sai ya sauya kundin tsarin mulki domin fara wa’adi na 3 abinda ya jefa kasar cikin rikicin siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.