Shugaban Twitter ya yi murabus saboda matsin lamba

Shugaban kamfanin sada zumuntar intanet na Twitter, Jack Dorsey  ya sauka daga mukaminsa, sama da shekara daya da tsallake rijiya da baya  da ya yi, bayan da wani dan gwagwarmaya mai hannun jari a kamfanin ya jagoranci yunkurin tsige shi.

Dorsey, wanda shi ne shugaban kamfanin hada-hadar kudade na Square ya shiga cikin matsin lamba  a shekarar 2020 daga hukmumomin kamfanin Elliott, wadanda suka bayyana damuwar cewa ya mamaye ko ina, kuma ayyuka na yi masa yawa ta wajen tafiyar da kamfanoni 2.

A wata sanarwa, Dorsey ya ce ya yanke shawarar yin murabus  ne  la’akari da cewa  kamfanin ya shirya ci gaba da harkokinsa ba tare da wadanda suka assasa shi ba.

Kamfanin ya ce yanzu shugaban bangaren injiniyoyinsa, Parag Agrawal ne zai maye gurbin Dorsey, inda tuni shugaban mai barin gado ya bayyana kwarin gwiwarsa a kansa.

Dorsey zai ci gaba da kasancewa mamba a majalisar zartaswar kamfanin har zuwa shekarar 2022 lokacin da wa’adinsa zai kare a yayin taron masu hannun jarin kamfanin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *