Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ya yi wa gwamnatin kasar kwarya-kwaryan garambawul, inda ya damka ragamar Ma’aikatar Cikin Gida a hannun tsohon Ministan Manyan Ayyuka Hamadou Adamou Souley tare da sauya wa na cikin gida Alkache Alhada wuri zuwa Ma’aikatar Kasuwanci.
Sauyin dai ya faru kwanaki biyu bayan da wata tarzomar nuna kin jin sojin Faransa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 3 tare da raunata wasu akalla 18 a garin Tera da ke yammacin kasar.
Kadayake sanarwar da kafafen yada labaran kasar suka fitar, ba ta yi bayani karara kan musabbabbin gudanar da garambawul din ba, amma a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP, hukumomin kasar sun ce, da dama ana dakon aukuwar daukar matakin tun ma kafin faruwar tarzomar Tera.
Sauran Ministocin da aka yi wa garanbawul sun hada da Ministan Shari’a, Boubacar Hassan wanda Ikta Aboulaye Mohamed ya maye gurbinsa.