Neymar zai yi jinyar makwanni 8

Dan wasan PSG Neymar zai yi zaman jinyar makwani takwas biyo bayan raunin da ya samu a wuyan kafarsa kamar yadda kungiyar ta birnin Paris ta tabbatar.

Neymar mai shekaru 26 ya samu raunin ne a wasan da PSG ta doke Saint-Etienne da kwallaye 3-1 a ranar Lahadi, abin da ya sa aka yi waje da shi akan gadon daukar majinyata.

Yanzu haka dan wasan mai shekaru 29 zai rasa damar buga wasanni bakwai da PSG za ta yi a gasar Lig 1 da kuma gasar cin kofin zakarun Turai.

PSG za ta fafata da Club Bruges a gida a ranar 7 ga watan Disamba a gasar cin kofin zakarun Turai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *