Messi ya lashe Ballon d’Or a karo na bakwai

Lionel Messi ya lashe kyautar Ballon d’Or da ake bai wa gwarzon dan wasan kwallon kafa da ya fi nuna bajinta a shekara, inda ya doke abokan takararsa Robert Lewandowski da Karim Banzema wajen lashe kyautar.

A karo na bakwai kenan da Messi ke lashe Ballon d’Or, yayin da yake ganin cewa, nasarar lashe wa kasarsa ta Argentina gasar kofin Kudancin Amurka, ita ce, ta sanya aka mika masa kyautar a bana.

An dai gudanar da bikin bada kyautar ce a Paris, birnin da ya bayyana a matsayin gida a gare shi jim kadan da komawarsa PSG don ci gaba da murza tamola bayan ya raba gari da Barcelona a cikin watan Agusta.

Masana harkar tamola a duniya sun bayyana cewa, babu wanda ya cancaci lashe Ballon d’Or a bara sama da Lewandowski, na Bayern Munich amma aka soke bikin bada ita saboda annobar Korona.

A bana dai, Lewandowski ne ya zo na biyu a jerin wadanda suka fi iya taka leda, sai Jorginho na Chelsea da ya yi na uku, yayin da Benzema na Real Madrid ya yi na hudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *