An kirkiri sabuwar fasashar maganin masu satar fage

A yau Talata ne, za a fara gwajin fasashar da ke dada taimaka wa alkalai yanke hukunci game da satar fage  da ‘yan wasan kwallon kafa ke yi.

Za a yi gwajin ne a gasar cin kofin kasashen Larabawa ta Arab Cup da hukumar kwallon kafa ta duniya ke shiryawa.

Sabuwar fasahar na dauke da kyamarorin daukar hoto guda 10 zuwa 12, kuma suna da karfin tattara bayanan dan wasa har guda 29 kuma sau 50 a cikin sakan daya.

Da zaran wannan fasahar ta gano alamar satar fage, nan take za ta aike da sako zuwa ga na’urar bidiyon VAR wadda ke yanke hukuncin karshe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *