‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da Ibrahim Aliyu Ishaq, DPO na ‘Yan Sandan dake kula da karamar hukumar Etsako ta Tsakiya dake Jihar Edo a Najeriya, sun bukaci a biya su diyyar naira miliyan 50 kafin su sake shi.
Rahotanni sun ce an sace baturen ‘Yan Sandan ne a karshen mako lokacin da yake tafiya a cikin motarsa akan hanyar Auchi zuwa Agenebode.
Ya zuwa yanzu rundunar ‚Yan Sandan Jihar bata ce komai dangane da bukatar ‚Yan bindigar ba.
Satar mutane domin kudin fansa da kuma kai hare-hare tare da kisan mutane da cin zarafinsu da ‚yan bindiga ke yi a Najeriya na cigaba da zama matsalar dake kann gaba wajen ci musu tuwo a kwarya a sassan kasar, musamman ma a yankin arewa maso yammacin kasar.
A watannin baya bayan nan ne kuma, lamarin yayi kamari inda, ‘yan bindigar suka rika afkawa makarantu suna sace dalibai da malamansu, lamarin da ya kai kan jami’an tsaro a yanzu.