Yan bindiga sun kai hari gidan yarin Jos dake Filato

Hukumar kula da gidan yarin Najeriya tace yanzu haka jami’an ta tare da na wasu hukumomin tsaro sun yi kawanya ga wasu yan bindigar da suka kai hari gidan yarin Jos.

Sanarwar da Kwantrola Janar na hukumar dake Najeriya ya bayar ta hannun kakakin sa Francis Enobore yace Yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 5.20 na yammacin yau, inda suka dinga harbi da bindiga har suka shiga ciki.

Gidan yari © CC0 Pixabay/Contributeur

Enobore yace jami’an su sun nemi taimakon wasu hukumomin tsaro inda suka yiwa gidan yarin kawanya, kuma ana kyautata zaton Yan bindigar na ciki.Jami’in yace nan gaba zasu yiwa jama’a bayanin halin da ake ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *