Dan wasan gaba na Leicester City, Jamie Vardy, ya kafa tarihin zama kafada kafada da tsohon dan wasan Arsenal Ian Wright, wanda ya fi yawan zura kwallaye a tsakanin ‘yan wasan da suka haura shekaru 30 a gasar Premier.
Dan wasan na Ingila ya samu nasarar ce bayan ci wa Leicester City kwallaye biyu a ranar Lahadi a wasan da suka doke Watford da kwallaye 4-2.
Dan wasan mai shekaru 34 a yanzu yana da kwallaye bakwai a gasar Frimiyar bana, yayin da kuma a dunkule ya zura kwallaye 127 a gasar Premier, kuma 93 daga ciki ya zura su ne bayan cika shekaru 30 da haihuwa.
Zalika Jumillar kwallayen 127 da Vardy ya ci a Firimiyar ya sanya shi zama na 14 wajen yawan kwallayen aa tarihin Firimiyar, inda yayi kunnen doki da Jimmy Floyd Hasselbaink, ya kuma sha gaban Robbie Keane da Nicolas Anelka.