Faransa ta jagoranci taron kasashen Turai kan matsalar ‘yan ci rani

Faransa ta karbi bakuncin wasu ministocin kasashen Turai domin tattaunawa kan hanyoyin dakatar da ‘yan ci-ranin dake tsallaka mashigin ruwanta da nufin shiga Birtaniya.

Sai dai Faransa ba ta gayyaci Birtaniya a zaman ba saboda sabanin da ke tsakanin kasashen biyu.

A ranar Lahadi, ministocin dake kula da kaurar jama’a na kasashen Faransa da Jamus da Netherlands da Belgium suka gana a tashar jiragen ruwa ta Calais dake yankin arewacin Faransa, inda suka tattauna kan hanyoyin magance matsalar safarar jama’a da ke samun taimako daga wasu ‘yan jagaliya masu samar wa ‘yan ci-ranin kananan jiragen ratsawa cikin Birtaniya ta mashigin ruwan na Faransa.

An dai shirya wannan tattaunawar ce biyo bayan mutuwar ‘yan ci-rani 27 a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da suke kokarin shiga Birtaniya daga Faransa a cikin wani karamin kwale-kwale da ya motse a tsakiyar teku saboda rashin iska, ga kuma tsananin sanyi da ake tafkawa.

Wasu gungun bakin haure sama da 40 cikin wani karamin kwale-kwale da ake hurawa, yayin barin gabar tekun arewacin Faransa don tsallakawa zuwa Ingila. 24 ga Nuwamba 2021. REUTERS – GONZALO FUENTES

Daya daga cikin mataimaka ga Ministan Cikin Gidan Faransa, Gerald Darmanin, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, manufar taron ita ce, inganta aikin hadin guiwa wajen yaki da safarar mutane.

Tun da farko dai, an tsara cewa, wannan tattaunawa za ta gudana ne tsakanin Darmanin da takwararsa ta Birtaniya, Priti Patel bayan kasashen biyu sun yi alkawarin daukar mataki jim kadan da mutuwar ‘yan ci-ranin.

Sai dai a cikin sa’o’i 48 da aukuwar hadarin, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya zargi Firaministan Birtaniya Boris Johnson da rashin mayar da hankali, lamarin da ya dada sukurkutata alakarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.