United ta tuntubi tsohon kocin Schalke 04

Rahotanni daga majiyoyi kwarara sun ce Manchester United na shirin nada tsohon kocin kungiyar Schalke 04 Ralf Rangnick a matsayin mai horas da ‘yan wasanta na wucin gadi har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Wani labari da kafar watsa labaran wasanni ta ‘The Athletic’ ta buga, ya ce Rangnick ya cimma yarjejeniyar karbar aikin horas da ‘yan wasan United na tsawon watanni shida, bayan kammala wa’adin kuma zai fara aikin baiwa kungiyar shawarwari na tsawon shekaru biyu.

Ana sa ran aikin Michael Carrick dake zama kocin rikon kwarya a yanzu zai zo karshe bayan karawar da za su yi da Chelsea a ranar Lahadi.

A halin yanzu dai United na matsayi na 8 da maki 17 a teburin gasar Firimiya, maki 12 tsakaninta da Chelsea dake jagorantar gasar ta bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published.