Tottenhan na cikin matsala kuma gashi ni ba mai sihiri bane – Conte

Kocin Tottenham, Antonio Conte ya ce babu shakkah kungiyar tasa na cikin matsala, inda ya kara da cewar shi fa ba mai sihiri ba ne da zai kawo karshen kalubalen da suke fuskanta nan take.

Conte ya bayyana haka ne bayan rashin nasara ta farko yayi tun bayan karbar ragamar horas da Tottenham, inda a daren jiya Alhamis NS Mura daga kasar Solvenia ta doke kungiyar sa a gasar cin kofin Europa.

Kocin ya kuma koka kan yadda tawagar ‘yan wasansa ta rasa karsashi tun farkon fara wasan, inda a cikin mintuna 11 na farko takwarorinsu na NS Mura suka zura musu kwallo a raga.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Harry Kane ya farkewar Tottenham kwallon, amma kuma ana gaf da tashi dan wasan Mura mai suna Marosa ya kara cin kwallo ta biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *