Kungiyar Paris Saint-Germain ta gana da Zinedine Zidane mai shekaru 49 domin kulla yarjejeniya da shi a matsayin sabon kocinta.
Bayanai sun ce Zidane da wakilan PSG sun gana ne a Royal Monceau daya daga cikin otal-otal mafi girma a birnin Paris.
Jaridar Le Parisien ta ruwaito cewa daga cikin wadanda suka gana da Zidane akwai daraktan wasannin PSG Leonardo da kuma Jean-Claude Blanc, babban manajan kungiyar wanda kuma amini ne ga Zidane.
Wannan tattaunawa dai ta jefa makomar kocin PSG na yanzu Mauricio Pochettino cikin hali na rashin tabbas, wanda tuni ya soma fuskantar suka kan rashin tabuka abin kirki a gasar zakarun Turai a wannan kakar, musamman ma a wasan baya bayan nan da suka buga da Manchester City, wadda ta lallasa su da 2-1 a ranar Laraba.