Nijar na yunkurin bunkasa noma domin ciyar da kan ta – Bazoum

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sha alwashin bunkasa harkokin noma da kiwo da zummar samar da abincin da zai wadata jama’ar cikin kasar da kuma wadanda ke kasashen makota.

Shugaban kasa Bazoum Mohammed ya bayyana haka lokacin da yake jawabi wajen taron bikin makon manoma dake gudana a garin Margou ta Jihar Dosso, wanda ya samu halartar manoma da makiyaya daga sassan kasar.

Bazoum ya bayyana cewar wani binciken masana da aka gudanar bisa tsari ya nuna cewar ‘Yankin kudancin Nijar daga Dogon Dutse zuwa Gaya da Boboye da Filinge da Margu na da eka miliyan 2 da za’a iya noman rani da damina saboda ruwan da ake da shi kwance a karkahsin kasa da yawan sa ya kai gangan biliyan 600.

Shugaban kasar yace idan gwamnati ta taimakawa manoma da makiyaya da kudin tallafi da kuma tsarin da zasu ci moriyar ruwan, Nijar zata iya ciyar da jama’ar ta da kuma ’yankin Afirka da Yamma.

Saboda haka Bazoum yace gwamnati zata tsaya da kafafun ta wajen ganin ta taimakawa manoman da makiyaya samun tallafin da suke bukata wajen bunkasa sana’ar su wadda zata kaiga daga darajar Jamhuriyar Nijar a idan duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.