Makomar kudaden tallafin mai ya janyo muhawara a ciki da wajen Najeriya

Shirin kawo karshen tallafin man fetur da kuma karkatar da kudaden tallafin zuwa ga rabawa marasa karfi domin rage musu radadin da za su fuskanta, na cigaba da haifar da muhawara a ciki da wajen Najeriya.

Shirin gwamnatin Najeriyar na tallafawa talakawa da rabon kudin dai zai rika lakume akalla naira tiriliyan 2 da biliyan 400 a duk shekara.

Yayin karin bayani kan shirin, ministar kudin Najeriya Zainab Ahmed ta ce gwamnati za ta rabawa mutane akalla miliyan 40 naira dubu biyar-biyar a kowanne wata, shirin da zai fara daga watan Yuli na shekarar 2022, lokacin da tallafin man fetur din zai kare.

Masu iya magana dai sun ce “ba cinya ba kafar baya” domin kuwa a yayinda gwamnatin Najeriyar ke yiwa ‘yan kasa wannan albishir, wasu kuwa fargaba suka bayyana kan ba lallai bane kudaden tallafin su isa ga jama’a, musamman marasa karfin da akai nufin saukakawa halin da za su shiga.

Sai dai kuma ministar kudin Najeriya Zainab Ahmed ta ce gwamnati za ta tabbatar da biyan kudaden ga wadanda suka cancanta ta hanyar amfani da lambobin tantancewa da katin shaidar dan kasa, da kuma lambar asusun banki, kuma za a aiwatar da shirin ne tare da hadin gwiwar Bankin Duniya.

A halin yanzu tallafin man fetur na lakume kusan naira biliyan 250 a kowane wata.

Wani rahoton kwararru ya nuna cewar Najeriya ke kan gaba wajen yawan matalauta a duniya, ko kuma marasa karfin da suke rayuwa kan kasa da dala kusan biyu a duk rana, abinda ya sanya wasu ke ganin za a samu sauki idan har shirin rabawa mutane miliyan 40 nairar dubu biyar-biyar duk wata ya samu nasara.

To amma, wasu kwararrun kuma a gefe guda sun yi gargadin cewa, shirin raba tallafin kudin na naira tiriliyan 2 da biliyan 400 a duk shekara ka iya zama wani sabon nauyin babba kan gwamnatin Najeriya, zalika duk wanda yam aye gurbinsa mai yiwuwa ya fuskanci kalubalen ci gaba da aiwatar da shirin ko kuma soke shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *