Kotun ICC ta rage hukuncin daurin shekaru 9 kan mai ikirarin Jihadi

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC a ta rage tsaurin hukuncin zaman gidan Yari da tsawon shekaru 2 da aka yanke wa dan kasar Mali Ahmad al-Faqi al-Mahdi mai ikirarin jihadi, saboda rawar da ya taka wajen rusa wuraren ibada a garin Timbuktu.

Cikin wata sanarwa, kotun ICC ta ce kwamitin da ya kunshi alkalai uku ne ya yanke shawarar rage hukuncin na daurin shekaru 9 a gidan Yari zuwa hukuncin daurin shekaru 7, abinda ke nufin lokacin da hukuncin daurin zai kammala akan Mahdi zai kama ne a ranar 18 ga watan Satumban shekarar 2022.

Al-Mahdi shi ne mutum na farko da kotun duniya ta ICC ta zartas wa hukunci kan samunsa da aikata laifukan yaki ta hanyar kai hari kan al’adun gargajiyar al’ummar kasar Mali, inda ya lalata wurin tarihi na hukumar UNESCO a Timbuktu.

A shekarar 2015 ne dai mai laifin ya mika kansa ga kotu aka kuma yanke masa hukunci a shekarar 2016.

A watan oktoban da ya gabata ne kuma Mahdi ya nemi afuwa kan barnar da aka yi, inda ya bukaci alkalai da su sake shi daga gidan yari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *