Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaron kasar da su kawo karshen barazanar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna, da ma sauran matsalolin tsaron da ake fuskanta a sassan kasar.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis din da ta gabata a karshen taron kwamitin tsaron Najeriya, wanda ya gudana a karkashin jagorancin shugaba Buhari a Abuja.