Amurka ta haramta kasuwanci tsakaninta da karin kamfanonin China 12

Gwamnatin Amurka ta kara wasu kamfanoni 12 na kasar China cikin jerin wadanda ta kakabawa takunkumin haramta kasuwanci da su, matakin da ta ce ta dauka saboda dalilai na tsaron kasa da kuma manufofin kasashen waje.

Amurka ta ce wasu daga cikin kamfanonin suna taimakawa wajen tsarawa tare da bunkasa shirin na’urorin kimiyya domin karfafa ayyukan sojojin kasar ta China.

Matakin Amurkan dai ya zo ne a daidai lokacin da ake samun takun saka tsakaninta da kasar ta Sin dangane da matsayi ko ‘yancin Taiwan da kuma wasu batutuwa kan manufofin kasashen ketare.

Ma’aikatar kula da kasuwanci ta Amurka ta kara da cewar an kuma maka karin wasu mutane da hukumomi 16 da ke aiki a China da Pakistan cikin jerin sunayen wadanda aka laftawa takunkumi saboda shiga cikin “shirin ayyukan nukiliya da kuma kera makamai masu linzami na kasar Pakistan, wanda manyan kasashen duniya basu aminta da shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *