Yawan haihuwa ya hana mu ci gaba a Nijar – Gwamnati

A jamhuriyar Nijar, yanzu haka sarakunan gargajiya daga sassan kasar na halartar wani taro domin tattaunawa kan yadda za a rage yawan haihuwa a kasar, wanda gwamnati ke cewa shi ne babban dalilin da ke hana wa Nijar samun ci gaba.

Shugaba Mohamed Bazoum ne ya jagoranci taron, inda ya jaddada matsayin gwamnatinsa na ganin cewa mata sun rage haihuwa a kasar.

Wannan taro, ina da kyakkyawan fatan cewa zai taimaka wa mata wajen daidaita rayuwarsu tare da amfanin ‘yayan da za su haifa da kuma makomarsu. inji shugaba Bazoum.

Shugaban ya kara da cewa, “kamar yadda na taba fada a can baya, matukar muna haihuwar ‘yaya barkatai, to lalle za mu gaza daukar dawainiyar ilmantar da su, idan har muka gaza ilmantar da su kuwa, to a nasu bangaren za su haifi ‘yayan da za su kasance dalilin gaza habbaka tattalin arziki balantana samar wa kanmu ci gaba.”

Alkaluma sun tabbatar da cewa matukar ‘yaya mata suka samu ilimi na akalla karamar sakandare, to ko shakka babu su ne za su fi taimakawa wajen samar da ci gaba a cewar shugaban na Nijar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *