Manchester United ta tuntubi Valverde don bashi aikin horarwa

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fara tuntubar tsohon kocin Barcelona Ernesto Valverde a wani yunkuri na bashi ragamar jagorancin kungiyar na wucin gadi.

Valverde mai shekaru 57 na cikin jerin manajojin da United ke son dauka don rike aikin wucin gadi kafin karshen kaka bayan raba gari da Ole Gunnar Solskjaer.

Yanzu haka dai tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar Micheal Carrick da ke cikin tawagar masu horarwa ne ke jagorancin United din yayinda ake ci gaba da laluben manajan rikon kwarya.

Duk da cewa United ta sanar da jerin wadanda ta ke shirin damkawa ragamar kungiyar ciki har da Mauricio Pochettino na PSG alamu na nuna abu ne mai wuya kungiyar ta iya daukar wani koci cikin sauki a ‘yan tsakanin nan musamman bayan kalaman Pochettico na jiya talata da ke cewa ya na farin ciki a kungiyar tasa kalaman da ya musanta rade-radin cewa shi ne zai maye gurbin Solskjear.

Leave a Reply

Your email address will not be published.