Babangida ya jinjinawa sojin Najeriya wajen yaki da ‘Yan ta’adda

Tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana goyan bayan sa ga jagorancin shugaban rundunar sojin kasa Laftanar Janar Faruk Yahaya na shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi kasar.

Babangida yace duk da yake Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro a wasu sassan kasar, rundunar sojin ta bada gagarumar gudumawa wajen tinkarar su tunda aka nada sabon babban hafsan sojin.

Shima a nashi bangare, tsohon shugaban kasa Janar Abdusalami Abubakar ya bayyana gamsuwa da irin rawar da shugaban sojin ke takawa wajen magance matsalolin tsaron da suka mamaye sassan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *