Algeria za ta janye tallafin kayakin masarufi bayan shawarar IMF

Gwamnatin Algeria ta sanar da shirin janye tallafin kayakin masarufi sakamakon raguwar kudaden shigarta daga bangaren makamashi a wani yunkuri na kaucewa fuskantar gibi a kasafin kudin kasar.

Matakin cire tallafin na Algeria ya biyo bayan bukatar hakan daga asusun bada lamuni na Duniya IMF da ke ganin ta wannan hanyar ne kadai kasar za ta ceto kanta daga matsalar tattalin arziki.

Tuni dai masana tattalin arziki suka goyi bayan matakin gwamnatin sai dai akwai fargaba yiwuwar janye tallafin ya haddasa tsadar rayuwa tare da tunzura matalauta da ke dogara da tallafin wajen tafiyar da rayuwarsu yau da kullum.

Kasar ta arewacin Afrika tattalin arzikinta ya dogara ne da albarkatun man fetur da iskar gas yayinda ta shafe shekaru wajen sanya tallafi a kusan ilahirin kayakin masarufin da al’ummar kasar ke siya baya ga man fetur da lantarki gabanin fuskantar matsalar tattalin arziki a bana.

A watan jiya ne asusun bada lamuni na IMF ya bukaci Algeria ta janye tallafin don ceto tattalin arzikinta wanda ya fuskanci koma baya tun bayan annobar covid-19.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *