Sojoji sun yi wa ‘yan bindiga luguden wuta a Sokoto

Rahotanni daga jihar Sokoto ta Najeriya na cewa jiragen yakin soji sun yi luguden wutan kan sansanonin ‘yan bindigar daji da suka buwayi yankin arewa maso yammacin kasar. 

Majiyoyin samun labarai na cewa tun ranar Asabar da ta gabata, sojin saman suka yi ta kai samame sansanonin ‘yan bindigar masu barna a yankin da ke kan iyaka da jihar Niger, kuma ana kyautata zaton ‘yan bindigar da dama sun gamu da ajalinsu.

Bayanai na cewa, an kai wani harin kan sansanin ‘yan bindigar a yankin Dan-Isa, inda tsagerun suka kwashe makwanni suna ta ta’asa a yankin.

Wani ganau a yankin ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, shakka babu an kashe ‘yan bindiga babu adadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *