A Jamhuriyar Nijar, shugabanin al’umma da tsoffin ‘yan tawaye sun nuna adawarsu da duk wani yunkuri na kafa kungiyoyin sa-kai don kare jama’a daga hare-haren ‘yan bindiga.
Ko a cikin makon da ya gabata, ‘yan ta’adda sun kai hari tare da kashe ‘yan sa-kai akalla 25 a garin Bakorat da ke yankin Tillia na jihar Tawa.