Matan shugabannin Afrika sun kammala taronsu a Abuja

Matan shugabannin kasashen Afirka, sun kawo karshen taronsu karo 9 a birnin Abuja da ke tarayyar Najeriya, taron da ya tattauna dangane da batutuwa da dama ciki har da sha’anin tsaro.

A karshen taron dai, matan shugabannin na Afirka, sun zabi uwargidan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hajiya Aisha Muhammadu Buhari a matsayin sabuwar shugabar kungiyar na tsawon shekaru biyu masu zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *